Harin Homs Shirin Bata Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ne - Staffan de Mistura

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a yunkurin sasanta rikicin Syria, Staffan de Mistura

Wakilin Gwamnatin Syria dake a yunkurin sasanta rikicin kasar ya ce, ya yarda cewa mummunan harin da aka kai a birnin Homs ranar Asabar an kai ne da nufin lalata shirin zaman lafiyan da aka cimma.

Bashar Al-Ja’afari ya shaidawa manema labarai “bama baman da 'yan ta’adda suka tayar a birnin Homs sako ne ga Geneva daga masu daukar nauyin 'yan ta’adda, kuma muna son sanarwa kowa cewa mun sami sakon kuma ba zamu bar wannan al’amari haka ba."

Ja’afari ya hadu da tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura a Geneva, inda de Mistura ya fadawa manema yada labarai kafin zaman tattaunawar cewa ya na fatan harin ba zai shafi batun zaman lafiyar ba.

Bayan zaman tattaunawar , Ja’afari ya bukaci wakilan 'yan adawa a teburin sasantawar da su yi Allah wadai da wannan hari a matsayin alkawarinsu na samar da zaman lafiya.

A bangarensu kuma 'yan tawayen sun yi alkawarin ci gaba da zaman tattaunawar.

Amma sun kalubalanci gwamnati da kokarin yi musu zagon kasa domin neman wasu bukatu daga wajen su.