Lauyoyin gwamnatin kasar Jamus sun ce masu bincike sun gano shaidar cewa mutumin da aka kama dangane da harin bam din da aka kai akan bas din dake jigilar 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Dortmund ya na da hannu a harin.
WASHINGTON D.C. —
Amma wata sanarwa na cewa suna bukatar izini ko kuma umarnin kama mutumin mai suna Abdul Beset A. bisa zarge-zagen cewa shi wakilin kungiyar ISIS ne.
Lauyoyin gwamnati sun ce sun yi imanin cewa Abdul ne ya jagoranci 'yan yakin sa kai guda goma, wadanda suke da hannu a sace mutane da yin fasa-kori da kuma karkashe mutane a gidansa kafin ya tsallaka zuwa Turkiya a shekarar 2015
A farkon makon nan ne wasu bama-bamai uku suka tashi a kusa da motar dake dauke da 'yan wasan Borrusia Dortmund yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa karawa da kungiyar Atletico Madrid.
Wannan hari ya yi sanadin raunata dan wasan kungiyar Marc Bartra a hanu lamarin da ya sa har sai da aka yi mai aiki.