Harin Boko Haram: Sojojin Najeriya Sun Karyata Adadin Mace-mace

Wasu sojojin Najeriya a bakin aiki

A cigaba da samun cikas da sojojin Najeriya ke yi a yakinsu da Boko Haram, rahotanni na nuna cewa 'yan Boko Haran sun kashe da dama daga cikin sojojin Najeriya, to amma rundunar sojan Najeriya ta ce sojojin Najeriya da aka kashe ba su kai yadda ake fadi ba.

Rundunar sojojin Najeriya ta amsa cewa lallai ‘yan Boko Haram sun kashe wasu sojojin Najeriya to amma yawansu bai kai yadda ake ta fadi ba. A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin ta ce lalle kam
mayakan Boko Haram sun kai hari akan dakarunta da ke Bataliya ta 157 a
Metele dake jihar Borno, amma akwai karin Gishiri bisa yadda ake ta
zuguguta wannan labari. Tunda farko dai jaridun Najeriya sun ruwaito
cewa mayakan na Boko Haram sun kashe sojoji fiye da dari.

Abin dai da ya fi tada hankalin ‘yan Najeriya shi ne yadda rahotanni ke
cewa mayakan na Boko Haram sun yi shigar burtu, inda su ka zo sansanin sojojin
Najeriyar a shiga irin ta yan uwa abokan aiki, har bayan da suka isa
ofishin kwamandan bataliyar kana suka fara bude wuta, abin da masanin
tsaro Wing Commander Musa Isa Salman ke cewa akwai sakaci.

mazauna shiyyar Arewa maso Gabas, na cewa hare haren bayannan da boko haram ta zafafa na tayar
masu da hankali, inda suke kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya kara
zage damtse wajen dakile koma bayan da ake samu a halin yanzu.

Ga dai wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rundunar Sojin Najeriya Ta Ce An Yi Karin Gishiri a Rahoton Kashe Sojoji Da Boko Haram su ka yi