Harin Bam Ya Kashe Mutane Hudu a Maiduguri

Wani hari da Boko Haram ta kai a Maiduguri a bara

Rahotanni daga birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sun ce wasu mutane hudu sun rasa rayukansu, bayn da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai hari a wata unguwa mai suna Sajeri.

Akalla mutane 13 ne suka sa mu raunuka kamar yadda wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya ruwaito.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe bakwai na daren jiya Asabar, inda wasu mutane uku suka shiga cikin taron jama’a suka ta da bama baman.

Kimanin makwanni biyu da suka gabata an samu wasu hare-hare ma a unguwar, wadanda suka halaka mutane da dama suka kuma jikkatu wasu.

Domin jin karin bayani kan wannan labari, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu da ya aiko daga Maiduguri:

Your browser doesn’t support HTML5

Bam Ya Halaka Mutane Hudu a Maiduguri - '3:47"