Hare-Haren Mayakan Saman Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda A Tafkin Chadi

An cimma wannan nasara ne sakamakon gudunmowar da sashen mayakan sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “Operation Hadin Kai” ya bayar a Asabar din data gabata.

Hare-haren rundunar mayakan saman Najeriiya sun hallaka ‘yan ta’adda a zirin Jubillaram dake shiyar Tumbuns na tafkin Chadi da yayi kaurin suna.

Sanarwar da daraktan hulda da jama’a da yada labaran shelkwatar rundunar, Air Commodore Olusola Akinboyewa ya fitar a yau Litinin tace an cimma wannan nasara ne sakamakon gudunmowar da sashen mayakan sama na aikin wanzar da zaman lafiya na “operation hadin kai” ya bayar a asabar din data gabata.

Akinboyewa ya kara da cewa Jubibillaram ya kasance ma’adanar abinci kuma maboya ga kwamandoji da mayakan ‘yan ta’adda.

“A baya bayanan sirri sun alakanta ‘yan ta’addar dake yankin da hare-haren da aka kai a baya-bayan nan, ciki harda harin daka kaiwa sojoji a garin Kareto a ranar 16 ga watan Nuwambar da muke ciki.

“A martaninta, jiragen yakin rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) sun kaddamar da zafafan hare-haren bam, da suka lalata gine-ginen da ake amfani dasu a matsayin ma’adana tare da hallaka ‘yan ta’addar dake wurin. Samamen daurayar da aka kai da bindigogin atilare sun tabbatar da hallaka gabadayan ‘yan tada kayar bayan dake kokarin arcewa daga yankin.”