Malaman addinin Musulunci sun yi tir da hare-haren da aka kai a wuraren ibada a garin Potiskum na jahar Yobe da kuma Jos Fadar gwamnatin jahar Filato. Su k ace wannan harin tsabar rashin Imani ne ya haddasa shi.
Walkilinmu a jahar Naija Mustapha Nasiru Batsari ya ruwaito Mataimakin Shugaban Izalatul bid’a Wa’ikamatus Sunna na kasa Sheikh Yusuf Samobo Rigajukun na cewa ba karamin zunubi ba ne a kai hari ma wadanda bas u jib a bas u gani ba; musamman ma a lokacin azumi. Shieikh Rigachukun ya yi rokon Allah ya taimaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ‘yan Majalisa da mashawartansa su samu nasarar dakile wannan al’amarin.
Shi ma wani kusa a kungiyar ta Izala Sheikh Abubakar Giro Argungu ya jajanta ma wadanda hare-haren su ka rutsa da su ne sannan y ace sannan ya shawarci gwamnati cewa yadda gwamnati ke nuna kyaliya ga masu zuwa kasashen waje karatun addini na taka rawa wajen tashe-tashen hankula a kasar saboda idan mutane su ka je kasashen waje karatun addini su ka dawo ba tare da taimakon gwamnati ba, wanda hakan ke hana gwamnati damar ta cewa game da irin abin da aka karanto daga kasashen waje. Y ace ya kamata gwamnati ta yi ruwa da tsaki game da dawainiya da kuma akidar masu karatun addini a kasashen waje. Y ace ya kamata gwamnatin Najeriya ta bullo da wani tsari inda za ta kasance da ikon ta cewa game da duk masallaci da cocicoci da sauran wuraren da ake tarurruka.
Shi kuwa wani dan kasuwa mai suna Alhaji Lawali Shukura kokawa ya yi kan yadda tashen-tashen hankulan ke lahani ga kasuwanci da kuma sauran muhimman harkoki a arewacin Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5