A yau Talata, Koriya ta Kudu ta gargadi makwabciyarta ta arewa, kan yunkurin harba roka mai tafiyar dogon zango.
Wannan gargadi na zuwa ne kwana guda bayan da hukumomin Pyongyong suka ambata cewa mai yiwuwa su harba tauraron dan adam, a lokacin wani muhimmin biki da ya shafi siyasar kasar a wata mai zuwa.
A cewar Koriya ta Kudu, wannan mataki, yunkuri ne na neman tsokana, wanda ya keta dokar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya haramtawa Koriya ta Arewa gudanar da gwajin makami mai linzami, kamar yadda Kakakin shugaban Koriya ta Kudu Kim- Min- seok ya ce.
Sai dai Kim ya kara da cewa, har yanzu Seoul ba ta ga wata alama da ke nuna cewa Pyongyong na shirin kaddamar da harba makamin.
Amma a jiya litinin jami’an Koriya ta Arewan sun sha alwashin za su kadamar da wannan shiri, wanda suka ce na’urar tauraron dan adama ce da za ta taimaka wajen karantar yanayi.