Shugabar ‘yan adawa a Belarus Sviatlana Tsikhanouskaya, ta yi kira ga Kungiyar Tarayyar Turai ta EU da kada ta amince da zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya gabata, wanda ta ce “an tafka magudi” a cikinsa, zaben da ta sha kaye a hannun dadadden shugaban kasar mai ci Alexander Lukashenko.
Cikin wani sakon bidiyo da ta aika gabanin babban taron da kungiyar ta EU za ta fara a yau Laraba, Tsikhanouskaya ta ce, “Lukashenko ba shi da wani iko a kasar da sauran kasashen duniya.”
Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna cewa Lukashenko ya samun kashi 80 cikin 100 na kuri’un da aka kada inda ya yi watsi da ikrarin da ake yi cewa an tafka magudi.
Ita kuwa abokiyar hamayyarsa ta ki amincewa da sakamakon zaben kamar yadda su ma zanga zanga suka yi, wadanda suka rika yin taruka a sassan kasar domin nuna adawa da shugaba Lukasheknko.