Har Yanzu Yahaya Bello Ya Ki Ba Da Kai Bori Ya Hau

Babban Kotun Tarayya a Legas

Tsohon gwamnan Jihar Kogi dake yankin arewa maso tsakiyar Najeriya, Yahaya Bello, har ya zuwa wannan lokaci, yaki ya bayyana gaban kuliya, tun bayan da Hukumar Dake Yaki da Cin Hanci Da Rashawa a Najeriya EFCC ta shigar da kara wata babban kotun tarayya dake Abuja a ranar 14 ga watan Maris na 2024, karkashin shugabancin mai Shari'a Emeka Nwite bisa zargin shi da aikata laifufuka 19, ciki har da karkatar da kudaden al'umma Jihar sama da naira biliyan 80 a tsawon shekaru 8 da yayi yana mulkin Jihar ta Kogi.

Kotun ta bukaci ya gabatar da kanshi, inda hukumar yaki da tu'annati da tattalin arzikin kasa, wato EFCC.

Yahaya Bello dai yayi batan dabo tun bayan lokacin da EFCC ta gabbayce shi don amsa tambayoyi amma yayi kunnen uwar shegu. Ya zuwa wannan lokaci, sau biyar kenan tsohon gwamnan ya bijirewa umurnin kotun wace ta bukace shi ya bayyana gabanta don wanke kansa daga tuhume tuhumen da hukumar ta EFCC ta keyi masa, duk da cewa tuni hukumar ta bayyana Yaha Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

A saurari rahoton Danasabe Ahmad:

Your browser doesn’t support HTML5

EFCC VS GYB.mp3