Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi yana daya daga cikin malaman da ke da dimbin mabiya a Najeriya. Sannan shine wanda ya gaji mahaifinsa Sheikh Abubakar Mahmud Gumi wajen gabatar da tafsirin Alkur’ani a masallacin Sultan Bello dake unguwar sarkin musulmi a Kadunar Najeriya.
Dakta Gumi yace har yanzu mutanen Najeriya na bukatar ci gaba da addu’a domin kuwa ita ce Allah ya karba ya kawo canjin gwamnati. A baya dai Dakta Ahmad din yace duk wanda aka sa a yanayin da ake ciki a Najeriya zai iya cin zabe daga Arewa.
Ya jaddada cewa da ace ta shawararsa ne da Buharin zai hakura ne ya barwa matasan da za’a sa a gaba a tarbiyyantar da su akan mulki. Ya kawo misalin yadda shugabannin irin su Barack Obama ma tarbiyya ya samu har yake jagorantar Amurka.
Sannan ya yaba yadda Allah cikin ikonsa Jonathan ya rungumi kaddarar yadda zaben ya kasance. Ya kuma yi kira ga jama’a cewa ba murna ake yiba addu’a ya kamata aci gaba da ita game da samun kyakkyawar makoma.
A hirar tasa da ma’aikacinmu Usman Ahmad Kabara, Daktan ya nuna cewa, lallai baya goyon bayan wani dan siyasa amma yana son ganin anyi abinda ya dace domin tun farkon shugabanci a hannun malamai ma aka sanshi.
Ya fadi haka ne da aka tambayeshi yadda yake son tsoma baki a sha’anin siyasa da kuma zargin yana marawa Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso baya ne fiye da shi Muhammadu Buhari yasa yace bai dace Buhari da Jonathan su ya fito takarar ba.
Your browser doesn’t support HTML5