Har Yanzu Ba A Samu Dan Wasan Kwallon Kafa Da Ya Kai Pele Ba - Farouk Yarma

Pele ya yi bankwana da duniya

Masu sha'awar kwallon kafa da ma sauran jama'a a fadin duniya na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil , Pele.

Yayin da masoya kwallon kafa a fadin duniya ke nuna juyayin mutuwar shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Pele na Brazil, masanin harkokin kwallon kafa, Malam Farouk Yarma, ya ce har yanzu ba a samu wanda ya kama kafar Pele ba a duk ‘yan kwallon kafa da ke raye da ma wadanda rai ya yi halinsa.

Farouk Yarma wanda shugaban wata cibiyar horar da ‘yan kwallon kafa ne mai taken YARMALIGHT,” ya ce ya gamu da Pele sau biyu inda a na karshen a 2018 su ka gamu a Rasha.

SOCCER-PELE/

Yarma ya kara da cewa duk zakarun kwallon kafa na duniya irin su Maradona, Zidane zuwa Messi sau daya su ka taba jagorantar kasashen su wajen lashe kofin duniya amma Pele ya samu nasarar yin hakan har sau uku.

SOCCER-PELE/GOALS

Farouk Yarma ya ce Pele dai jigo ne a harkar kwallon kafa da zai cigaba da zama abun koyi da misali a tsaknin ‘yan wasa har ma wadanda za su zo nan gaba.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Mutuwar PELE.mp3