Masu Zanga Zanga Sun Janye a Ofishin Jakadancin Amurka

Kungiyoyin masu bore da Iran ke marawa baya, wadanda suka mamaye ofishin jakadancin Amurka a Iraqi, sun janye daga harabar ofishin, bayan da suka kwashe kwana biyu suna zanga zanga a wurin.

Hakan na faru ne, yayin da hukumomin Tehran da takwarorin aikinsu na Washington ke jefawa juna kalamai masu cike da barazana.

Gabannin hakan, jami’an tsaron Amurka sun yi ta amfani da borkonon tsohuwa da harsashen roba akan daruruwan masu zanga zangar, a lokacin da suke ta jefa duwatsu akan ginin ofishin jakadancin na Amurka da ke Bagadaza, babban binin kasar ta Iraqi.

Masu zanga zangar, sun fara boren ne a ranar Lahadin da ta gabata, domin nuna fushinsu kan wasu hare-haren sama da dakarun Amurka suka kai, akan mambobin kungiyar Kataeb Hezbolla masu ta-da kayar baya.

Amurka ta ce hare-haren martani ne kan kashe wani ma’aikacin kwantiraginta da mayakan suka yi a makon da ya gabata.