Ana Ci Gaba Da Neman Sauran Mutanen Da Hatsarin Kwale-kwale Ya Rutsa Da Su A Kwara

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq

Rahotanni sun yi nuni da cewa mutum sama da 100 ne suka rasa rayukansu a hatsarin wanda ya auku a ranar Litinin.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya jajintawa al’ummar Patigi a game da ibtila’in hatsarin kwale-kwalen da ya auku wanda ya yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane yayin da har yanzu ba a gano wasu da dama daga cikin mutanen ba.

Kwale-kwalen wanda daga cikin wadanda suke cikinsa, yana dauke da mutane daga wasu jihohi, ya taso daga Egboti a jihar Niger kan hanyarsa zuwa Kpada a karamar hukumar Patigi a jihar kwara.

A wata sanarwa a da ya fitar a ranar Talata, gwamnan ya bayyana bakin cikinsa a game da samun rahoton aukuwar hatsarin kwale-kwalen wanda ya rutsa da mutane da dama, musamman ma mazauna Ebu, Dzakan, Kpada, Kuchalu da Sampi duka a karkashin karamar hukumar Patigi.

Bayan nan, gwamnan ya ce zai ci gaba da bibiyar aikin ceton da tuni aka fara gudanarwa tun daren ranar Litinin

Ya jijinawa sarkin Patigi Etsu Parigi mai martaba Alh. Ibrahim Umar Bologi II da sauran kananna hukumomi da irin kokarin da suke yi wajen ceto masu tsawon rai wadanda suka kaucewa aukuwar kaucewa aukuwar al’amarin.

Mutane sun koma sufuri ta hanyar ruwa wanda suke gani ya fi tafiya a mota sauki bayan da man fetur ya yi tsada a dalilin cire tallafin man fetur da sabon gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Ko da yake, irin wannan tafiya na tattare da hadurra musamman a lokacin damuna domin ruwa rafi da tekuna suna haurawa.