Har Yanzu Ana Neman a Rage Kudin Tafiya Aikin Haji

  • Ladan Ayawa

Wasu 'yan Najeriya a lokacin sallar idi

Yayin da ake shirin fara jigilar alhazan Najeriya zuwa kasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana, kwamaitin dake kula da ayyukan hajjin a majalisar wakilan kasar ya ce zai kara gabatar da bukatar neman a rage kudin wannan farali wanda aka kara a wannan shekara.

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya dake sa ido kan ayyuka hajji, ya gudanar da wani taro inda ya yanke shawarar kai ziyara wajen mukaddashin shugaban kasa Yemi Osibanjo, domin neman a rage kudin hajjin bani da ya yi tashin gwauron zabi.

Kudin wannan shekara da hukumar alhazan Najeriya ta saka ya kai Naira miliyan 1.5 wanda ya haura sama da yadda abinda aka biya a bara.

Hukumomin kasar sun ce tashin farashin dala ne ya tilasta karin.

A ranar 30 ga wannan wata ake sa ran fara aikin jigilar alhazan daga Najeriya, lamarin da wasu suke ganin lokaci ya kure.

A tattaunawarsu da wakilin Sashen Hausa na Muryuar Amurka, Nasir Adamu El-Hikaya daya daga cikin ‘yan majilisar wakilai a Najeriya, Mohammed Bago wanda mamba ne a kwamitin wucin gadi, ya yi mai karin haske kan matakin da suke so su dauka na zuwa wajen mukaddashin shugaban kasa.

Amma ya fara tambayarsa shin yana ganin za su iya samun wata nasara akan wannan batu ganin cewa lokacin wannan tafiya ya kawo jiki?

Ga Dai Nasirun da ci gaban wannan tattaunawar.

Your browser doesn’t support HTML5

Har Yanzu Ana Neman a rage Kudin Tafiya Aikin Hajji- 2'59