Babu alamun sassautawa a rikici da ke tsakanin dakarun Indiya da na China a kan iyakar da su ke takaddama a arewacin Himalayas. Amma duk da yake manyan kasashen biyu na yankin Asiya sun tura dakaru da kuma manyan bindigogin yaki zuwa yankin, tattaunawa tana gudana a matakin sojoji da diflomasiyya don a warware tashin hanakali, a cewar jami’an Indiya.
“Akwai sojojin China da dama a wurin,” Ministan Tsaron Indiya, Rajnath Singh, ya fadawa gidan talabijin Channel na Indiya a ranar Talata, inda ya tabbatar da zuwan sojojin a kan iyaka. Duk abinda ya kamata mu yi, Indiya ta riga ta yi.
Manyan wuraren da aka ja daga su ne kusa da kwarin Galwan da Tafkin Pangong Tso a Ladakh wanda ke kula da samun dama na zuwa wurare masu matukar muhimmanci na kan iyakar Himilayan.
Jami’ai a New Delhi sun fadawa kafar yada labaran yankin cewa sojojin China sun shigo cikin yankin Indiya ta wurare uku daban-daban, sun kafa tantuna da matsugunan tsaro da ya saka Indiya zuwa wurin.