Har Yanzu Akwai Fargabar Ambaliyar Ruwa A Wasu Sassan Najeriya.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan jihar Jigawa kwanan baya

Yayin da aka yi bankwana da ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya, har yanzu akwai fargabar wannan matsalar da dangoginta a sassan Najeriya

Duk da a wasu sassan Najeriya, musamman arewacin arewa, an kwan biyu da dakatawar ruwan sama, amma har yanzu a wasu sassan a na samun ruwan kamar da bakin kwarya.

Baya ga fargabar cigaba da samun ambaliya, ruwan da kan zo daidai lokacin da manoma ke tattara amfaninsu, ka iya shafar amfanin gonan.

Tabka gaggarumin ruwan sama da aka yi a Abuja a Jumma’ar nan ya kara nuna gaskiyar hasashen ruwan sama ka iya kaiwa har watan gobe.

Har yanzu wasu sassan Najeriya na fuskantar yiwuwar ambaliyar ruwa

Rahotanni na nuna har yanzu akwai wadanda amfanin gonarsu, kamar wake, ba su gama nuna ba ko su na yin fure, ta yadda idan an samu ruwan sama a irin wannan lokacin su kan zubar da furen, a wayi gari da tarin harawar wake ba waken.

Hasashen aukuwar irin wannan yanayi, ya sa hukumar kula da hasahen yanayin ta Najeriya NIMET kaddamar da wata manhajar wayar salula da ta kan turawa mutane bayanai don sanin halin da a ke ciki.

Farfesa Mansur Bako Matazu shi ne shugaban hukumar “binciken da mu ka gabatar ya nuna cewa akalla a kasar nan akwai layukan waya wajen miliyan 170…kuma ya fi sauki da a ce sako da za a aika a takarda ko a bayanai na tsakanin hukumomi. In akwai yanayi na ruwan sama mai tsanani ko tsawa ko iska mai karfi ko za a samu fari a cikin damuna du mu na aika wannan sako.”

Masani kan lamuran sauyin yanayi Hussaini Dauda ya zayyana abubuwan da kan faru a sanadiyyar yawan ruwa matukar ba matakai hukumomi da jama’a su ka dauka ba.

Har yanzu wasu sassan Najeriya na fuskantar yiwuwar ambaliyar ruwa

Hussaini Dauda ya kawo batun zaizaiyar kasa, ambaliyar ruwa da kuma yanda mutane kan toshe magudanan ruwa da shara da kan zama babbar illa ga muhalli.

A bana dai mutane da yawa sun koma gona musamman sassan da a ka samu sassaucin kaluablen tsaro irin na Boko Haram a arewa maso gabar amma tsadar taki ta sa wasu manoman na cewa tamkar ka karba da hannun dama ne ka mika da na hagu.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Ruwa, zaizayar kasa, da ambaliyar ruwa a Najeriya