Ministan ayyuka da gidaje na Najeriya Babatunde Raji Fashola, ya ce za a kammala hanyar nan da za ta hade Abuja har Birnin Algiers, cikin shekaru uku masu zuwa.
Duk da yake ministan ya ce hanyar zata ratsa kasashe da dama irin Nijar da Mali da Najeriyar, hakan bai hana wasu dari-dari da batun ba. A bangare daya dai wasu na cewa a daidai lokacin da gwamnatin Buhari ya kamata ta bi batun gyara hanyoyin cikin gida da ke fama da ramuka shi ne za ta tado da wannan batu? Misali hanyar Minna zuwa Kontagora da hanyar Numan na Adamawa zuwa Jalingo.
A cewar ministan lokacin da yake magana da manema labaru, “Matsala ita ce kanun labaru, adalci shi ne ku nuna ba dukkan hanyoyin ke da muni ba, hakki na kan ku na baiyanawa ‘yan Najeriya da mu ke amfani da kudin harajinsu cewa akwai aikin da a ke gudanarwa.“
Masana irinsu Dakta Kole Shetima na asusun Mcarthur, ya ce a tunaninsa, idan mutane suna shakkun wannan magana ba laifi ba ne ba saboda hanyoyin cikin gida ma ba a samu an ingantasu ba.
Ga karin bayani a cikin sauti daga Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5