Siyasar shekara ta 2023, dai siyasa ce dake fuskantar sauya shaka. A baya bayan nan, gwamnan jihar Ebonyi Dave Omahi, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Kawo yanzu dai ana cigaba da samun manyan 'yan siyasa dake sauya sheka inda bayanai suka nuna cewar, a majalisar Dattawan Najeriya, a kalla sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga jami’iya mai mulki ta APC zuwa PDP mai adawa. Daga ciki kuwa har da Sanata Francis Alimikhena daga jihar Edo, dake kudancin kasar.
Muryar Amurka ta ji ta bakin wani dan jihar Shimee Silvanus, dangane da wannan dambarwa inda yace "Mafi yawacin 'yan daban daban ba ayi masu adalci ba a yayin zaben fitar da gwani da ya gabata ina ganin wannan shine babban dalili da yasa suke ficewa daga jam’iyya zuwa wata jam’iyyar. Haka kuma wasu 'yan siyasa suna sauya sheka saboda ra’ayin su ba don ra’ayin jama’a su ba."
Shima wani dan takarar gwamna kuma jigo a jam’iyyar APC Alh. Abubakar A. A. Gumbi ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Ku Duba Wannan Ma Zamu Iya Hada Kai Da Wasu Jam'iyyu Don Lashe Zaben 2023- KwankwasoAlh. Abubakar A. A. Gumbi ya ce "mun yanke shawara ni da jama’a ta a APC mu koma jami’iyar PDP kuma babban dalilin mu shine rashin adalci da kuma rashin iya gudanar da mulki, kuma wanda ke jagorantar APC kamar ba dan siyasa bane abinda dan siyasa ke bai wa kowa hakkinsa."
Mun kuma tuntubi mai sharhi kan harkokin siyasa Prof. Yahaya Tanko baba shugaban sashen nazarin kimiyar siyasa a jamiar Usmanu Dan Fodiyo ko yaya suke kallom sauya sheka da yan siyasa keyi a yanzu.
A cewarsa wannan abu ne wanda ake hasashe musaman ma ganin cewar kamin a gudanar da zabuka na jam’iyyu tare da zaben fidda gwani akwai riginginmu da yawa a mataki na kasa da na gwamnoni da na 'yan majalisu, da kuma abinda ya shafi takarar shugaban kasa.
Saurari cikakken rahoton Abubakar Lamido Sakkwato cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5