A Nijar, hukumar zaben kasar CENI, tayi kira ga 'yan hamayyar su kai zuciya nesa, su taho a hada kai a gudanar da zabe zagaye na biyu, domin ci gaban kasar da tsarin salon mulkin demokuradiyya.
Mataimakin shugaban hukumar zaben na farko Umaru Sanda, wanda yayi wannan kira, yace duk da cewa sunji 'yan hamayya suna cewa zasu kauracewa zaben, har yanzu a hukumance basu gaya musu ba.
Mohammed Sani Muhamman, wanda shine kakakin dan takarar jam'iyyar Moden Fa Lumana, ya tabbatar da cewa dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar Hamma Amadou, zai shiga takarar, sabanin abunda aka ji a baya.
Duk da haka yace, jam'iyyar da kuma gamayyar jam'iyun hamayya da ake kira KOPA, sun janye wakilansu daga hukumar zabe ta CENI, kuma ba zasu fito ranar zabe ba.
Kakakin jam'iyyar ta Moden Fa Lumana, yace muddin hukumomin kasar suka ci gaba da tsare Hamma Amadou, 'yan hamayya zasu kauracewa zaben.
Ga karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5