Halin Da Kasuwannin Hannayen Jarin Duniya Ke Ciki

Dakin da ake hada-hadar hannayen jarin Amurka a New York.

Kasuwannin Asiya a yau Litinin sunyi kyau sakamakon kyakyawar fatar masu zuba jari game da batun farfadowar kasuwanci bayan kaucewar annobar coronavirus.

Hannayen jarin kamfanin Japan Nikkie ya rufe da karin maki 2.2%. Hannayen jarin Hang Seng da ke Hong Kong shi ma ya dada armashi da kashi 0.5% da maraicin kasuwanci, kana, Shanghai Composite ya cirra da maki 1.7% cikin dari.

A Australiya, hannayen jarin S&P da ASX suma sun cirra da maki 0.8%. Sai hannayen jarin KOSPI da ke koriya ta Kudu ya cirra da maki 1.6%, kana TSEC da ke Taiwan yayi sama da 1.1%. Hannayen jarin SENSEX da ke Mumbai ya cirra da maki 0.3% cikin dari.

Wasu mutane a Hong Kong a gaban wani talabijin mai nuna halin da kasuwannin hannayen karin ke ciki

A kasuwar mai ana siyar da danyen man Amurka akan farashi dallar Amurka $40.14 kowace ganga, abin da ke nufin yayi kasa da kashi daya cikin dari.

Kana ana siyar da danyen man BRENT a kasuwar duniya akan farashi dallar Amurka $42.88 kowace ganga, wato yayi kasa da maki 0.8%.

Hannayen jarin dukkanin manyan kamfanonin Amurka dai sunyi amarshi.