Ba yabo ba fallasa dai a kasuwannin hannayen Jarin Asiya a yau Alhamis, al'amarin da ya kawo karshen wata zabura da su ka yi, saboda zaton za a samu farfadowar tattalin arziki bayan annobar COVID-19 ta kau.
Kamfanin Nikkei a Tokyo ya fadi da digo 4 cikin dari a karkshen kasuwanci, yayin da hannayen jarin HANG SENG dake Hong Kong yayi kasa da digo 2 cikin dari, kana SHANGHAI COMPOSITE ya cira da digo daya cikin dari da maraicin kasuwanci.
A wani wuri a yankin kuma, hannayen jarin S&Pda ASX dake Sydney yayi kasa da digo 9 cikin dari, KOSPI dake SEOUL kuma, yayi kasa da digo 3 cikin dari, inda TSEC dake Taiwan ya cira da digo 1 cikin dari, sai SENSEX dake Mubai kuma, ya haura da digo 7 cikin dari.
Kasuwannnin Turai ma sun bude cikin jinkiri, inda FTSE dake London yayi kasa da digo 5 cikin dari, CACA-40 dake Paris kuma yayi kasa da kashi 7 cikin dari, sannan, DAX dake Frankfurt, yayi kasa da kasha digo 2 cikin dari.
Kasuwannin duniya a farkon makon nan, sunyi armashi bayan da babban bankin Amurka da na Japan su ka yi alkawarin sayen hannayen jarin kamfanoni domin farfado da tattalin arziki da annobar coronavirus ta durkusar.