An bukaci mata dasu tashi tsaye wajan neman na kansu a maimakon dogaro da iyaye ko mazajensu domin hakan zai taimaka gaya wajan kare masu mutunci, wata matashiya Amina Zubairu Yahya, ne ta bayana haka a wata hira da Dandalinvoa.
Tace hakan ya zama wajibi ganin irin kallon da ake yiwa matan arewa matasa kallon marasa harzaka a wuraren ayyukan mussamam ma kasancewarsu mata inji Amina Zubairu Yahya wata matashiya da ta ce tana fuskantar kalubalen kasancewarta mace kuma ma’aikaciya.
Ta ce ba ma a wajen aikin kadai ba hakan ya samo asaline tun daga karatun ta na jami’a, inda ta fara fuskantar kalubale da dama masamman daga malamai.
Ta kara da cewa a yayin da ta nemi karantar ilimin sanin albarkatun kasa bata samu ba sai aka bata kwas din harshen Turanci wato English ta fara fuskantar matsaloli daga malamai.
Da farko dai ta ce matsalar da ta samu shine wani malaminta ya nuna yana sonta, rashin amincewa masa ya jawo mata wasu tangarda, sannan bayan kamala karatun ta kuma da ta samu aiki sai ake mata kallon gazawa wanda ita a ganin ta take hakkin mata ne.
Amina ta kara da cewa sai an baiwa mace dama ne sannan za’a iya tantance gazawarta ko akasin haka, dukkuwa da cewar akwai wasu lokutan da mace ke da rauni.