Hajj 2019: Mahajjata Sun Yi Hawan Arfa

Mahajjata a hawan Arfa. APTOPIX Saudi Hajj

Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan musulunci da ake so Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwa, idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya.

Yayin da ake Hawan Arfa a yau Asabar, sama da Musulmai miliyan biyu ne suke gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya - kasa mafi tsarki ga mabiya addinin Islama.

Tun a jiya Juma’a aka fara gudanar da ayyukan hajjin, inda mahajjatan suka yi dawafi ko kuma zagaya Ka’aba sau bakwai.

Daga cikin sauran ayyukan da aikin hajjin ya kunsa, akwai tafiyar safa da marwa.

Akan kuma ziyarci wuraren tarihi a Makka da Madina.

Shi dai aikin hajji, yana daya daga cikin shika-shikan musulunci da ake so kowanne Musulmi ya yi, ko da sau daya ne a rayuwa, idan dai yana da hali da kuma koshin lafiya.