Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Manchester united zasu hadu a wasan kusa da karshe na wasannin zakarun Turai, yayin da Bayern Munich kuma zata kara da Atletico Madrid idan ta kai labari zuwa wasan karshe.
Madrid wadda ta yi wa kungiyar Wolfsburg kallon hadarin kaji a zagayen karshe ta tsallake zuwa wasan karshe na kakar wasan shekarar 2014, yayinda ita kuma Juventus ta nuna bajintar ta. Kungiyar ta sami nasarar lashe wasan tsakanin kakar wasa ta shekarar 2013 da 14 inda ta doke Atletico da ci 4 – 1 bayan Karin lokaci, yayin da Manchester city take sabuwa katakau a wasannin kusa da na karshe karo na farko.
Kungiyar ta kasa kai labari a zagaye na 16 a kakar wasa ta shekarar 2013-14, da kuma shekarar 2014 da 15, amma ta dan sami dama dama akan kungiyar Dynamo Kyiv da kungiyar Garmain.
Sau biyu kungiyar Madrid da Manchester city sukai karon batta, yayin da Madrid din ta lashe gasar sa’an nan tayi kunnen doki a sauran wasannin a lokacin da suka hadu a cikin rukunin kungiyoyin da suka shiga kakar wasannin shekarar 2012 da 13.
Kungiyar City zata amshi bakuncin Madrid ranar 26 ga watan Afirilu, Atletico kuma zata marabci kungiyar Bayern wan shekare, yayin da zata koma ranar 3 ga watan Mayu inda zasu taka leda a gida tare da Madrid ranar 4 ga watan Mayu.