A baya gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya zargi wasu ‘yan siyasar jihar mazauna Birnin Tarayya Abuja, da cewar su na yi wa jam’iyya da shi kansa zagon kasa, inda su ke fifita abokin takararsa Sanata Lado Danmarke akan shi da su ke jam’iyya daya.
Gwamna Aminu Bello Masari ya ambaci Hajiya Hadiza Bala Usman, shugabar hukumar kula da tashoshin ruwan Najeriya da Ministan Jiragen Sama Alhaji Hadi Sirika game da zargin yin zagon kasa. Wanda hakan ya sa Hadiza Bala Usman, ta maida martani game da zargin.
A hirar ta da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Hajiya Hadiza ta ce “Abin ya ba ni mamaki matuka, yadda aka zarge mu da wannan danyen aikin” ta ci gaba da cewa babu yadda za a yi ace mutum ya na jam’iyyarsa, amma ya je ya na taimaka wa wani da ke wata jam’iyya. Duk dai da cewar a rahoton nasu sun ce za su kafa kwamiti don ya binciki wannan zargin da ake yi.
Ta ce su na nan su na sa ido domin ganin sakamakon binciken, domin ganin irin hujjojin da za su nuna cewar sun yaudari jam’iyya, “wannan ba wani abu ba ne illa yarfen siyasa” sai ta kara da cewar “zan nemi gwamna Masari don jin asalin tushen wannan maganar.” Ta kara da cewa, "Babu wani dan jam’iyya da zai so a ce ya na yaudarar jam’iyyar da ta yi masa riga."
Akwai dangantaka mai kyau tsakani na da gwamna Masari, a cewar ta "domin kuwa mun yi aiki hannu da hannu" wajen ganin nasarar wannan gwamnatin a lokacin yakin neman zabe da ya gabata a farkon wannan shekarar. Ta ce, "Mu na waya lokaci zuwa lokaci. Don haka wannan rahoton ya ba ni mamaki kwarai da gaske."
Ta cigaba da cewa, "Babu kanshin gaskiya akan rade-radin cewar ina gyaran hanya don tsayawa takarar gwamna a zaben 2023, ko kadan wannan ba gaskiya ba ne, ba ni da muradin tsayawa takara ko kadan." Hajiya Hadiza ta kuma ce, " Idan har al’ummar jihar Katsina sun bukaci na tsaya, za mu tattauna da su, kuma zan nuna musu rashin alfanun tsayawa ta takara." Sannan ta ce, "Yanzu dai akwai sauran lokaci kafin a fara maganar siyasa.":
Saurari hirar cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5