Hadin Kan Sabbin Jami'an Tsaron Najeriya Shine Nasara

Shugaba Muhammadu Buhari

Kwararru a fanin tsaro da manyan ‘yan siyasa dama kungiyoyi masu zaman kansu sun fara bayyana ra’ayinsu game da sauyin da aka samu a bangaren tsaro.

Wasu na yabawa da sabbin jam’an tsaron da shugaba Buhari, ya nada saboda kwarewarsu, a wani bangare kuma wadansu na ganin da an rike tsofaffin har zuwa wani dan lokaci.

Wani kwararre a fanin tsaro Janar Saleh Maina, mai ritaya, ya bukaci sabbin jami’an tsaron dasu, yi nazarin tarihin rikici domin gano bakin zaren, su kuma hada kai na cikon ukku shine sanya kasar Najeriya a zukatansu.

Babban sakataren gudanarwar na jamiyyar SDP, DR. Sadik Umar Abubakar Gombe, yace nada ‘yan asalin shiyar arewa maso gabas, zai iya kawo karshen kalubalen tsaron, yace “Wannan ya nuna cewa Gwamnati ta fuskanci matsakar kuma a shirye take ta murkushe matsalar, saboda aka samu ‘yayan wadannan wurare sannan aka samu wadanda abokanan aikinsu sun tabbatar kwararru ne akan wannan yanayi.”