Wani matashin mawakin Hip hop, kuma dalibin jami’ar, Hussain Adam, ya ce abinda ya sa gaba a wakokinsa shine yadda kan al’umomin arewacin Najeriya, zai hade.
Yace ya fara wakar hip-hop ne domin fadakar da muhimmancin hadin kan ‘yan Arewa da zaman lafiya ganin cewar abinda yayi karanci Kenan a arewancin kasar.
Ya ce kasancewarsa dalibi, kuma mai kishin arewa ya sa ya fara waka, inda ya fi maida hankali ga harkar zaman lafiya da hadin kan juna baya ga nishadantarwa da kuma ilmantarwa.
Lil Hussy, kamar yadda lakaninsa yake, ya ce ba kamar sauran sassan kasar bane, wanda ya ce tsananin kishin arewa ne ya sa yake isar da sakonnin zaman lafiya da tunasar da ‘yan arewa cewar sai an hada kai ne sannan za’a samu zaman lafiya.
Ya kara da cewar kasancewar shi dalibi ne yana fuskantar matsaloli da suka shafi lamari na kudi mussamamam na wajen fitar da wakokinsa, kuma babban burinsa ya samu fice a kasa baki daya.
Your browser doesn’t support HTML5