Hadin Guiwar Aikin Soja Tsakanin Amurka Da Rasha Ba Zai Yiwu Ba

Jim Mattis

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis ya bayyana a taron kungiyar tsaro ta NATO da aka gudanar a birnin Brussels jiya alhamis cewa,  hadin kan ayyukan soja tsakanin Amurka da Rasha ba zai yi wu ba a halin yanzu saboda da yanayin bai dace ba.

Mattis ya fada a wani taron manema labarai da aka gudanar a shelkwatar kungiyar tsaron hadin gwiwa ta NATO cewa, “yanzu yanayin da muke ciki bai dace da hada hannu a fannin ayyukan soji ba.”

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi rauni mafi muni tun bayan zamanin yakin cacar-baki, saboda da zargin Moscow da ake yi da yin katsalandan a zabukan Amurka da kuma fin karfin da take nunawa Ukraine.

Mattis ya bayyana haka ne bayan da ministan harkokin tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu ya ce a shirye Moscow take ta sake maido da hadin kai da ma’aikatar tsaro ta Pentagon.