Hadarin Jirgin Sama Ya Halaka Mutum 12 a Kazakhstan

Hatsarin Jirgin Sama

Wani jirgin saman kasar Kazakhstan wanda ke dauke da mutum 90 ya yi hadari da safiyar yauJuma'a, jim kadan bayan tashinsa.

Mutum 12 ne dai suka rasa rayukansu, yayin da fiye da mutum 20 suka samu munanan raunuka a cewar hukumomin kasar.

Hatsarin Jirgin Sama

Hukumar harkokin sufurin jiragen saman farar hular kasar, ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar cewa, jirgin na kamfanin jiragen saman Bek Air ya buge wata katanga da wani gini mai hawa biyu bayan ya tashi daga filin jiragen saman Almaty.

Sakamakon haka, hukumomi suka dakatar da tashin dukkanin jiragen kamfanin na Bek Air da kuma jirage kirar Fokker 100 a kasar, har sai an gudanar da bincike kan lamarin.