Gamayyar shahararrun kamfanonin kimiyya da fasar zamani da suka hada da Google, Waymo, Lyft da Amazon, suna wani yunkuri na samar da motar Tasi mai sarrafa kanta. Kamfanonin suna son amfani da damar ne don kwace kasuwar kamfanin sufuri na Uber.
A jiyane hadakar kamfanonin suka sanar da cewar duk wani mutun mai manhajar kiran motar haya a wayar shi zai iya cin gajiyar wannan sabon tsarin. Shi dai sabon hadakar kamfani na Waymo zai fara aiki ne a watan Satunbar wannan shekarar.
Ita dai motar mai sarrafa kanta ta kamfanin Waymo, zata kasance tana dauke da matuki don duba yadda take gudanar da ayyukanta ba wai don shike tuka taba, da kuma kokarin kyara mata wasu abubuwa a dai-dai lokacin da matsala ta samu.
Samar da mutun a cikin motar zai kara bawa mutane karfin gwiwar shiga ba tare da wani fargaba ba. Kamfanoni na da yakin nin cewar ta haka ne kawai zasu iya samun karin kudaden shiga.