Hadakar Kungiyoyin Addinin Kirista da Na Musulunci Suka Yi Taron Rigakafin Rikci

Tambarin kasar Nger

Taron nasu sun shiryashi ne domin ya kawar da duk wata matsala da ka kaiga rikici tsakanin addinan biyu a kasar Niger

Ustaz Manik jagoran shirya taron yace addinin musulunci addini ne dake kira akan salama ba wai ga musulmi kawai ba. Ya kira musulmi da wanda ba musulmi ba su zauna lafiya.

Ya cigaba da cewa Allah ya koyawa musulmi kada yayi tashin hankali da wanda bai fitar dashi daga gidansa ba amma yayi adalci. Yace wadanda suke zaune dasu cikin Maradi da kasar Niger gaba daya suna kamanta adalci daidai gwargwado domin su zauna dasu lafiya. Domin haka wajibi ne ga musulmin Niger ya zauna dasu lafiya. Yana fata kada irin rigingimun dake faruwa a kasashen dake makwaftaka dasu ba zasu faru a Niger ba.

Shi ma Pastor Idris Sale na bangaren mabiya addinin kirista cewa yayi faduwa ce ta zo daidai da zama domin manufar tana da kyau domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Yace sun ga mahimmancin zaman lafiya domin sun ga wadanda ke da gidajensu amma sabili da babu zaman lafiya suna kwana kan duwatsu, wasu kuma suna cikin daji. Yace ya zama abun farin ciki garesu da suke da sauran zaman lafiya. Sabili da haka su rike zaman lafiya su kuma dauki matakan da zasu inganta zaman lafiyan har su ci ribarshi yadda Allah ya nufesu su ci rabar.

Ga rahoton Chuaibu Manni.

Your browser doesn’t support HTML5

Hadakar Kungiyoyin Addinin Kirista da Na Musulunci Suka Yi Taron Rigakafin Rikci - 2' 31"