Matasa muslmai na Jamhuriyar Nijar sun gudanar da taronsu na wannan shekarar a birnin Agadez, wanda ya zama taro na ishiri da biyu.
Ibrahim Seni wanda ya kasance shugaban matasan na duk kasar Nijar ya bayyana dalilansu na zaben Agadez.
Yana mai cewa kowace shekara su kan zabi birnin da zasu yi taonsu. Yace matasan sun kumshi mutane masu sana'a daban daban. Akwai ma'aikatan gwamnati. Akwai 'yan kasuwa da manoma da makiyaya da dai sauransu.
Inji Seni taron na da mahimmanci saboda a taro ne zasu tattauna abubuwa da dama.
Abubuwan da suka fi maida hankali kai a wannan taron sun hada da ayyukan jinkai da taimaka wa gajiyayyau, wa'azi ga matasa domin kada su kauce su shiga harkokin ta'adanci
A cewar Ibrahim Seni jahilci yake sa matasa shiga ayyukan ta'addanci. Abu na biyu kuma shi ne talauci. Idan mutum bashi da abun hannu kuma bashi da aiki idan wani ya zo da muguwar manufa ya bashi kudi sai ya sashi aikin da watakila bai dace. Rashin samun shawara daga dattawa ya kan sa matasa su kauce hanya. Ya kira iyaye kada su bar 'ya'yansu ba kulawa. Iyaye su kula da abubuwan da 'ya'yansu ke yi. Sun dinga sauraran 'ya'yansu tare da sanin abokanansu.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5