Hadakar kungiyar naksassu a Tarabar ta shirya zanga zanga

Masu Fama Nakasa

Hadakar kungiyar masu fama da nakasa a jihar Taraba da suka hada da kutare da kurame da guragu da makafi da bebaye sun yi wata gagarumar zanga zanga zuwa fadar gwamnatin jihar don ta share musu hawaye

Masu zanga zangar rike kwalaye masu rubutu dake jan hankali ga bukatunsu, sunyi maci zuwa ofishin gwamnan jihar Arch.Darius Dickson Isiyaku, inda kwamishiniyar harkokin mata Malama Loise Emmanuel ta amshi takardan kokensu.

Masu fama da nakasar sun ce suna bukatar gwamnatin jihar ta rika daukarsu aiki kamar yanda wasu jihohin ke yiwa mutanensu dake fama da nakasa saboda sun gaji da yawon barace barace. Sun kuma ce ana nuna musu wariya wurin daukarsu aiki, a binda yasa suka yi kira ga gwamnati ta kawo karshen wannan bambanci.

Kwamishina Loise Emmanuel, amadadin gwamnan jihar, ta basu hakuri tare da yi musu alkawarin za duba koken nasu. Tace a can baya ta bada umarni da a dauki wasu mata guda biyu masu fama da nakasa, maganar da ya tada hayaniya wanda ke tabbatar da masu zanga zangar basu lamunta da maganar ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba Disabled Demonstrate