Hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Nigeria ta janye umarnin korar yan kabilar Igbo bisa wasu sharudda

Taron Hadakar Kungiyar Matasan Arewa

Hadaddiyar kungiyar matasan arewacin Nigeria ta janye umarnin korar yan Kabilar Igbo daga arewacin kasar, amma ta gitta wasu sharudda.

Matasan arewacin Nigeria su dakatar ko kuma sun janye umarta 'yan kabilar Igbo su tashi daga arewa su koma yankinsu na kudu maso gabashin kasar kan ranar daya ga watan Oktoba.

A wani gagarumin taro a Abuja, hadaddiyar kungiyar matasan tace ta dau wannan mataki ne saboda kiraye kiraye da dattawan yankin suka yi da kuma yan kabilar Igbo masu son zaman lafiya da ci gaban kasancewar Nigeria dunkulalliyar kasa.

Daya daga cikin shugabanin kungiyar mai suna Nastura Ashir Sharif yace sun daidata da kungiyar gwamnonin arewa akan wannan lamari, in ka tsaida gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufai da yace a damke su.

Sa'anan kuma sun gitta wasu sharudda na janye wannan wa'adin. Ka'idodi sun hada da kama shugaban kungiyar rajin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu da gudanar da zaben raba gardama akan Biafra da rufe dukkan shagunan da suke sayar da kwayoyi masu sa maye, da ake zargin yan kabilar Igbo da yi a yankin arewa da kuma hukunta dukkan masu furta kalaman kiyaya.

Shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima daya halarci taron, yace matakin shin mafi ala. Haka kuma yace matasan sun nuna kauna ga kasar mu, kuma sun nuna daraja ga shugabani.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasan arewacin Nigeria sun janye wa'adin korar yan kabilar Igbo 2"54