An shawarshi matasa dasu hada makaranta da sana’a, idan har suna son jugewa zaman kashe wando, wata daliba wace ta hada makaranta da aiki Sabira Abubakar, ne ta bada shawarar a wata hira da wakiliyar Dandalinvoa.
Dalibar da ke aiki a wani shagon sayar da agogo, ta ce tana sana'ar ne a hannu guda kuma karantunta na diploma inda take karantar harkar kudi.
Ta ce tana zuwa shagon sana'arta a lokatun da bata zuwa makaranta a yunkurin ta na zama mai dogaro da kai.
Sabira ta ce lokaci yayi da mata matasa zasu zama masu dogaro da kai ta hanyar saukakawa iyaye wajen taimaka musu da kananun bukatun su.
Ta kara da cewa dalilin aikin da take yi ta daukewa iyayenta wasu dawainiyarta da suka hada da kudaden makaranta da wasu bukatu na ta.