A hada hadar ‘yan wasan kwallon kafa na duniya, Shahararran dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal kuma zakaran kwallon ka na yankin turai mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya amince daya kara tsawon kwantareginsa a kungiyar ta Real Madrid.
Ronaldo dan shekara talatin da daya da haihuwa kwantirakinsa zai karene a 2018, a yanzu ya amince zai kara shekaru ukku inda zai kammala a 2021, ana sa ran cewa sati mai zuwa zai rattaba hanu.
Ronaldo ya taho Real Madrid ne daga Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, a shekara ta 2009, ya taimaka wa kulob dinsa ta Real Madrid, wajan daukar kofin zakarun nahiyar turai wato (UCL) har sau biyu da kuma cin kofin La-liga na kasar Spain tun zuwansa ya kuma jefa kwallaye sama da dari uku da hamsin a wasanni daban daban da ya buga wa Real Madrid.
Cristiano zai biyo bayan takwaransa Gareth Bale, wanda ya rattaba hannu a satin da ta wuce na tsawon shekaru shida wa Kungiyar.
Shima dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal Mesul Ozil, na dab da rattaba hanu wa Kungiyar na tsawon shekaru biyar masu zuwa inda zai kammala a shekara ta 2021, Kungiyar ta Arsenal ta amince zata biyashi fam dubu £160,000 a duk sati.
Shi kuwa Dimitri Payet na Westham yace kofarsa a bude take ga duk wata kungiya mai sha'awarsa
Payet ya ce yana da niyyar barin kungiyarsa ta Westham a tsakiyar kakar wasan bana in haka ta kama.
Arsenal da Manchester United, na zawarcin dan wasan Atletico Madrid mai suna Jose Gimenez, akan kudi fam miliyan £54.
Manchester United ta saka kudi fam miliyan £70 domin sayen dan wasan Atletico Madrid, mai suna Antoine Griezmann.
WASHINGTON, DC —