A cigaba da hada hadar saye da sayarwar 'yan wasan kwallon kafar duniya da akeyi na shekarar 2019.
Kungiyar kwallon kafar Paris St-Germain tana yunkurin shiga gaban Juventus, wajan sayen dan wasan Tottenham Danny Rose, inda ake tsammanin cewar zata kammala cinikin dan wasan bisa darajar kudi fam miliyan 20.
A bangaren Mancherster United kuwa rahotanni na bayyana cewar shugaban kungiyar Ed Woodward, ba zai bi tawagar kungiyar zuwa wasannin share fage da take yi ba, saboda yana so ya kammala cinikayyar wasu 'yan wasan kafin a rufe saye da sayarwar 'yan wasa.
Woodward yace yana da kwarin gwiwar kammala sayen 'yan wasanni irin su Harry Maguire, dan wasan baya na Leicester da na matashin dan wasan tsakiya na Newcastle Sean Longstaff.
Shi kuwa shugaban kungiyar Tottenham Daniel Levy, ya bayyana cewa zai daga farashin dan wasan bayan su Toby Alderweireld, daga fam miliyan £25 zuwa fam miliyan £40 idan har babu wanda ya saye shi a farashin baya ba, nan da ranar Juma'a kamar yadda yarjejiniyar kwantiragin sa ta tanada.
Arsenal ta ce nan da makonni biyu masu zuwa ne mai horas da kungiyar Unai Emery, zai yanke shawarar ko zai amince ya saki matashin dan wasan Ingila Reiss Nelson, zuwa Hertha Berlin a matsayin aro ko kuma zai cigaba da zama da dan wasan.
Mai horas da Liverpool Jurgen Klopp har yanzu na bukatar karin sayen dan wasa daya kafin a rufe kasuwar, sai dai bincike ya nuna kulob din ba zai kashe kudi kamar na shekarar da ta gabata ba, inda suka kashe fam miliyan £170, a bangaren sayen 'yan wasa, sai dai kwalliya ta biya kudin sabulu, tunda ta samu nasarar lashe kofin zakarun turai (Uefa Champions League 2018/19) wanda shine karo na shida da kungiyar take lashe wa.
Bincike yana nuni da cewa cinikin dan wasan Manchester United da Real Madrid ke yi akan Paul Pogba mai shekara 26, zai dogara ne ga barin dan wasan gaba na Wales Gareth Bale, mai shekara 30 da haihuwa daga kungiyar ta Spain, wanda ake samun takun saka tsakanin sa da maihoras da kungiyar ta Real Madrid Zinade Zidane, kamar yadda wasu mujallu suka ruwaito.