Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya

Sunayen masu horas da ‘yan wasa wadanda hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF zata tantance domin daukar su aiki sun hada da

  1. Salisu Yusuf
  2. Tom Saintfiet
  3. Paul Le Guen.

Shugaban kwamitin tantancewar shine Mr Chris Green.

A bangaren hada hada da zawarcin zaratan ‘yan wasan kwallon kafa na duniya kuma, kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala sayen dan wasan Leister City mai suna N’Golo Kante dan shekaru 25 akan kudi fan miliyan 32 na tsawon shekaru 4.

Man united na zawarcin Fabinho dan shekaru 22 da haihuwa akan kudi fan miliyan 22, yayin da Liverpool ke neman dan wasan Barcelona Jeremy Mathiew mai shekaru 25 da haihuwa.

Kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Espanyol Vellareal, Valencia da kuma Evaton na zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Man United mai suna Juan Mata.