Hada Hadar Cinikaiya Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya

Liverpool ta sake dawowa kan batun ta na zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester united, Marouane Fellaini, 30 wanda PSG da Monaco ke sha'awar ganin sun dauko shi, kwantiraginsa zai kare a Manchester karshen kakar wasan bana.

Bayern Munich, ta ce zata bada dama ta sabunta kwantiragin 'yan wasanta Franck Ribery, mai shekaru 35, a duniya da Arjen Robben, dan shekaru 34 da haihuwa wanda kwantirakinsu zai kare a karshen kakar wasan bana

Har ila yau Kocin kungiyar Manchester united Mourinho, ya ce zai bukaci yin canji da 'yan wasan biyu Paul Pgoba, da Anthony Martial wanda duk kansu 'yan kasar faransa ne wajan karbar dan wasan gaba na Paris Saint-Germain dan kasar Brazil Neymar.

Ita kuwa kungiyar Paris Saint-Germain, tana da niyyar dauko dan wasan gaba na gefe daga Liverpool Mohammed Salah mai shekaru 25 da ya dawo kulob dinta da taka leda.

Kocin kungiyar Manchester city, Pep Guardiola, na shirin kasancewa Kocin da ya fi kowane Coach daukan kudi a duniyar kwallon Kafa, inda zai rika karbar fam miliyan £20 duk shekara a kungiyar Manchester city bisa sabuwar yarjejeniyar da zasu yi zuwa shekarar 2020.

Leicester City, tana shirin dauko dan wasan tsakiya na Norwich mai suna James Maddison, 21 akan kudi fam miliyan 17 in har dan wasanta dan kasar Algeria Riyad Mahrez, zai bar kungiyar a karshen kakar wasan Bana.

Everton ta shirya domin dauko dan wasan gefe na kungiyar Burnley, dan kasar Ireland mai suna Robbie Brady, 26.

Wata jarida mai suna Sun on Sunday ta wallafa cewar kungiyar Real madrid zata maye gurbin Kocinta Zinedine Zidane da Kocin Liverpool Jurgen Klopp in har sun Sallami Zidane.

Your browser doesn’t support HTML5

Hada Hadar Cinikaiya Da Musayar Zaratan 'Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya