Ministan tsaro na kasar Habasha ya sanar da kama madugun zanga zangar kin jinin gwamnati da ya addabi kasar, tare da jaddada cewa, jami’an gwamnatin tarayya dake dauke da makamai suna kokarin shawo kan tashin hankali ne. An sanar da mutuwar wadansu farin kaya kalilan a cikin kwanaki da dama da suka shige.
Siraj Fegessa ya fada a wani taron manema labarai jiya da aka yi a birnin Addis Ababa cewa, “Idan ba a kama irin wadannan mutanen ba, kayi tunanin irin barnar da za a yi.
Ya bayyana haka ne ‘yan sa’oi kafin isar sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a babban birnin kasar, kasa ta farko da ya yada zango a ziyarar mako guda da ya kai kasashen Afrika dake yankin Hamada.
Ya kai ziyarar ce da nufin jaddada bukatar yaki da ta’addanci, da yunkurin wanzar da zaman lafiya, da batun cinikayya da zuba jari da kuma shugabancin kwarai.
A cikin makon nan wata kungiyar matasa da ake kira Qeerroo ta jagorancin wani yajin kwanaki uku a yankin Oromiya suka toshe hanyoyi tare da kira ga cibiyoyin kasuwanci su rufe, yayinda suke matsa lamba a saki dukkan fursunonin siyasa. An kawo karshen yajin ne da ya bazu daga Addis Ababa zuwa wadansu birane jiya Laraba.