Kasar Somaliya ta yi tir da abin da ta kira, “wani yinkuri na tozarta ta da gwamnatin kasar Habasha ta yi,” inda har jami’an tsaronta, su ka nemi dakatar da Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mahmud, daga shiga wurin taron Kasashen Afurka a birnin Addis Ababa, a cewar wani bayanin gwamnatin Somaliya jiya Asabar.
“Gwamnatin Tarayyar Somaliya ta yi matukar Allah wadai da yinkurin takala da gwamnatin Habasha ta yi, na kawo rudami ga tawagar Shugaban Somaliya, a hanyarta ta zuwa taron Kungiyar kasashen Afurka na 2024 a birnin Addis Ababa,” a cewar kamfanin dillancin labaran Gwamnatin Somaliya (SONNA).
“Wannan mataki ya saba ma dukkannin tsare tsaren harkokin diflomasiyya na kasa da kasa, musamman ma sanannun ka’idojin Kungiyar Kasashen Afurka. Wannan matakin, wani dori ne, a kan jerin matakai marasa kan gado, wadanda gwamnatin Habasha ta yi ta daukawa a baya bayan nan,” a cewar bayanin.
To saidai mai magana da yawun Firaministan Abiy Ahmed na Habasha, Billene Seynoum, ta gaya ma kafar labarai ta AFP cewa, Habasha ta yi kyakkyawar tarba ma Firmanista Mahmud, kuma ta ba shi cikakken girman da ake bai wa shugabannin kasashen da ke halartar taron.
Dama akwai wata jikakka tsakanin kasashen biyu, inda kasar Somaliya ke zargin kasar Habasha da rashin mutunta diyaucinta, saboda wata yarjejeniyar da aka cimma ranar 1 ga watan Janairu tsakanin Habashar da yankin Somaliland, wanda ya ayyana kansa a matsayin ‘yantacciyar kasa a 1991, tare da neman kasashen duniya su amince.