Amurka Ta Nanata Kudirin Yaki Da Cin Hanci A Nahiyar Afirka

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo

Gwamnatin kasar Amurka ta nanata kudirin ta na yaki da cin hanci a nahiyar Afirka. Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya bayyana hakan a ziyarar da ya kai a kasar Angola, daya daga cikin kasashen Afirka uku da yake ziyarta a nahiyar Afirka bayan kasashen Senegal da Habasha.

Sai dai kamar yadda aka saba daga kasar ta Amurka a yan shekarun baya, Najeriya bata cikin kasashen da sakatare Mike Pompeo zai kai ziyara, duk kuwa da mahinmancin kasar ta fuskar tattalin arziki, da kasuwanci a nahiyar, da kuma kasuwanci tsakanin ta da Amurka.

Tuni dai wannan matakin ya jawo sharhi tsakanin yan Najeriya, inda wasu
ke sukan kasar Amurka, amma wasu kuma ke ganin matsalar daga Najeriya ne

A kwanan nan ne Amurkan ta saka Najeriya cikin kasashen da za a sanyawa 'yan kasar takunkumin wani nau’in biza na zama cikin Amurka, dalilin zargin ayyukan ta’addanci, duk kuwa da cewa 'yan Najeriya basu da alaka ta kud da kud da duk wasu nauyin ta’addanci ga kasar ta Amurka.

Mikail Shagarda wani mazaunin Legas ya ce gaskiya matakin hana biza, Amurka tana la’akari ne da bayanan da ta samu kuma ya rage ga Najeriya
tabi hanyoyin da suka dace na magance wannan matsalar.

Ziyarar ta Pompeo a Afirka dai ya maida hankali akan bunkasa tattalin arziki da tsaro, daya daga cikin matsalolin dake ciwa Najeriya tuwo a kwarya. Koda yake a ganawar da shugaba Muhammadu Buhari yayi da shugaba Donald Trump na Amurka a bara, sun amince sayarwa Najeriya wasu zaratan jiragen yaki da kuma sauran taimako ta fuskar tsaro.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko anan gaba kasar Amurka zata sassauto da manufofinta tsakanin ta da Najeriya.

A saurari rahoton Babangida Jibril sauti Lagos, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwanmnatin Amurka Ta Nanata Kudirin Yaki Da Cin Hanci A Nahiyar Afirka