Gwamnonin Kano Da Jigawa Sun Bayyana Shirinsu

  • Ibrahim Garba

Jam'iyyar APC ta su Shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu Buhari ce ta ci Kano da Jigawa

Gwamnonin Kano da Jigawa za su cigaba da ayyukan da gwamnonin yanzu su ke yi inbanda abin da ba a rasa ba

Gwamnoni masu jiran gado na jihohin Kano da Jigawa sun fara bayyana abubuwan da za su fi ba su mahimmanci da zarar sun fara aiki. Yayin da Gwamnan jihar Kano mai jiran gado Abdullahi Umar Ganduje ke cewa, zai baiwa sha’anin ilimi fifiko, shi kuwa takwaran aikinsa sabon gwamnan Jigawa Badaru Abubakar yace noma zai baiwa kulawa, sai dai bakin gwamnonin biyu ya zo wuri guda wajen kammala dukkanin ayyukan da zasu gada.

Daga Kano wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya ruwaito gwamnan jihar Jigawa mai jiran gadon na cewa za a inganta noman rani da na damina ta yadda za a rinka kai amfanin gona daga jihar ta Jigawa zuwa wasu wurare har a samu riba sosai. Ya ce zai cigaba da ayyukan da aka fara a jihar Jigawa karkashin Sule Lamido saboda barn ace ace wai don kawai an canza gwamnati za a canza ayyukan da aka fara ko kuma a yi watsi da su.

Shi ma gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje cewa ya yi za su cigaba da gudanar da ayyukan da aka fara a gwamnati mai ci, kodayake y ace akwai wasu sabbin tunani da sabbin dabaru kan wasu batutuwa don inganta su. Ya ce ilimi ne zai samu fifiko saboda komai sai da iliminsa ake iya yi da kyau.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnonin Kano Da Jigawa Sun Bayyana Shirinsu