Duk ma'akatan gwamnati wakilan shugaban kasa ne da gwamnati da kasar gaba daya koina aka kaisu aiki.
Saboda haka su ma'aikatan wajibi ne su wakilci jama'a da jagorancin jama'a duk inda suke.
Taron zai nuna masu abubuwan da ake kyautata zaton zasu yi da abun da ake jira daka garesu saboda cimma alkawuran da shugaban kasa ya yiwa jama'a. Za'a fadakar dasu yadda zasu taimakawa shugaban kasa cika alkawuransa.
Maganar tsaro na cikin manyan kalubale da kasar ke fuskanta saboda haka wajibi ne tsaro ya zamo kan gaba a taron abubuwan da ma'aikatan zasu maida hankali kai.
An kira talakawa su kiyaye doka, su kuma ma'aikatan, da suka kasance wakilan gwamnati, kada su sa siyasa ko kawo banbancin siyasa a harkokin ayyukansu.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5