Dr Shettima Mustapha wanda yake jawabi a wani babban taron kasa da aka shiryawa kungiyoyi a Minna fadar gwamnatin jihar Neja yace sau da yawa sun sha tunkarar gwamnoni da bukatun a yi wani abu zahiri game da cigaban aikin gona a yankin arewacin Najeriya.
To saidai abun takaici har wa zuwa wannan lokaci babu wani abun azo a gani da ya bayyana. Dr Shettima Mustapha yace cikin shekarar 2001 shi da Audu Ogbe da Murtala Nyako sun je sun samu gwamnoni 19 a Kaduna. Sun gaya masu baro-baro cewa yadda abubuwa ke tafiya a wancan lokacin idan basu tallafawa ayyukan noma ba wata rana ma ba zasu iya biyan albashi ba.
Yace noma bai bunkasa a kasar ba. Idan ya bunkasa me yasa ana shigo da shinkafa da albasa ko man gyada daga wasu kasashen. Yace ba wai sai an yi karya ko fadanci akai ba. Babu ne. Idan akwai me yasa kasar na sayo kayan abinci daga waje. Surutu a kafar telibijan ba zai habaka ayyukan noma ba. A tsaya a yi aikin.
Lokacin da shugabannin kasar suka yi aikin anfanin gona ya rike kasar. Yanzu da kasar ta koma kan surutu a telebijan ai an ga abun dake faruwa.
A nashi gefen shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya gwamna Babangida Aliyu na jihar Neja mai masaukin baki ya bayyana mahimmancin kungiyoyin wajen cigaban tattalin arzikin kasa. Ya kara da cewa sanarwar bayan taron zai zabawa duk gwamnonin Najeriya ba na arewa ba kadai.
Makasudin taron dai shi ne wayar da kungiyoyi game da yadda za'a samu tallafi daga gwamnati da kuma yadda za'a tafiyar da tallafin da aka samu domin anfanin kungiyoyin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5