Gwamnoni Sun Nemi A Sauya Yadda Ake Rabon Arzikin Kasa

Gwamnoni a Najeriya sun nemi a sauya yadda ake rabon kudaden kasa idan har za su biya ma'aikatan su sabon mafi karancin albashin Naira 30,000 duk wata.

Batun biyan mafi karancin albashin Naira 30,000 duk wata ga ma'aikata wanda tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu, har ma wadansu jihohi suka fara biyan ma'aikatan su, sai dai har yanzu akwai jihohin da ba za su iya biya ba.

Lamarin da kwararre a fanin tattalin arzikin kasa da kasa, Yusha'u Aliyu, ya ce akwai matsala idan har wasu jihohi ba za su iya biyan albashin ba. Kuma ya na ganin gyara yadda ake rabon arzikin 'kasa zai dan taimaka, tunda wasu jihohi sun fi wasu karfin tattaln arziki, amma dai a yi taka tsantsan kar yin haka ya janyo wa gwanatin matsala.

To sai dai jigo a Jamiyyar APC kuma masanin shari'a, Barista Abdullahi Jalo, na ganin yunkurin ya yi dai-dai domin ai tun zamanin mulkin Obasanjo ne Majalisar kasa ta yi wannan doka, kuma dokar ta cancanci a yi mata gyara a yanzu, domin a samu ci gaba a kasa, kuma za a ce wanan Gwamnati ta yi rawar gani tunda zai shafi rayuwar al'ummar kasa.

Shi ma shugaban kungiyar gwamnoni na kasa kuma gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi, ya ce ba a taru an zama daya ba, wasu jihohi basu da karfin da wasu ke dashi, saboda haka akwai yarjejeniyar da gwamnatin tarraiya ta shiga da Kungiyar Kwadago, a wani fanni na mafi karancin albashin, wanda ba lallai ba ne jihohi su anince da hakan ba.

Ya ci gaba da cewa, suna kan bakar su na neman a sauya yadda ake rabon dukiyar kasa, wanda aka fara tun shekaru kusan 20 da suka wuce kuma tun lokacin ne gwamnonin ke kokawa akan haka, kuma dole ne su bi dokar da ta ce a biya ma'aikata, amma kuma za su ci gaba da neman a yi gyara da zai taimaka wa kasa.

Ga karin bayani a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnoni Sun Nemi A Sauya Yadda Ake Rabon Arzikin Kasa