Gwamnatin kasar Kamaru ta fitar da sanarwan cewa zata gudanar da zabubbuka hudu a cikin wannan shekarar.
Zabubbukar dai sun hada dana shugaban kasa, majilisar dokoki,Dattijai da kuma kananan hukumomi,kana ta fitar da cfa miliya 50 domin gudanar da wannan aikin.
Alhaji Rilwanu Sharubutu na jamiyya mai mulkin kasar ya shaidawa Muhamman Awal Garba cewa yanada kwarin gwiwa wannan zaben zai gudana.
Sai dai kuma a wuri daya ‘yan jamiyyar adawa sun bayyana shakkun su game da wannan zaben suna cewa kasar da bata zaune ciki kwanciyar hankali ake maganar zabe.
Alhaji Ibrahim Maiyaki na jamiyyar adawa ya shaidawa muryar Amurka cewa shugaban kasa shine wuka shine nama kuma ya fitar da wannan sanarwan ce domin ya kwantar wa mutane da hankali dama sauran kasashen duniya.
Ga Muhammam Awal Garba da Karin bayani.2’21
Your browser doesn’t support HTML5