Jami’an hukumar kula da kan iyakoki na Najeriya wato Nigeria Boundary Commission zasu fara shata iyakoki nan ba da jimawa ba.
WASHINGTON DC —
Hukumar shata iyakokin Najeriya ta jagoranci wani gangami a Jihar Binuwai da Taraba da nufin fadakar da mutane akan shirin da ta ke yi na fara shata iyaka tsakanin al'ummomin biyu.
Mataimakin gwamnan Jihar Binuwai Engr. Benson Abonu da takwaransa na Taraba Haruna Manu, shugabanin al’umman jukun da kuma na Tibi sun sha alwashin kawo karshen tashe-tashen hankulan dake faruwa kan iyaka a tsakanin al’ummomin jihohin biyu.
A fatan cewa, wannan aiki da za a gudanar, zai taimaka wajen samun fahimta tsakanin al'ummomin biyu ya kuma samar da zaman lafiya tsakaninsu.
A saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-Aziz:
Your browser doesn’t support HTML5