An shata kadada kusan dubu biyu da dari biyu a matsayin na gwaji a yankin Gumi inda babu madatsar ruwa.
Baicin gyarawa manoma kadadan domin shuka an basu bashin kayan aiki kaman ingantacen iri da maganin kwari da takin zamani da rijiyoyin burtsatse da injinan ban ruwa har da kudaden wasu ayyuka. Manoman kowa ya samu kudi abun da ya kama daga N180,000 zuwa N200,000 akan kowace kadada daya.
Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar yace shirin marawa ne ga kokarin gwamnatin tarayya na bunkasa sha'anin noma da wadata kasa da abinci. Yace idan Allah Ya yadda tsakanin wannan shekarar zuwa mai zuwa kasar zata daina shigo da shinkafa daga waje. Sauran jihohin ma sun tashi tsaye domin tabbatar da cewa an cimma burin gwamnatin tarayya.
Wasu manoma da suka anfana daga shirin sun yi furuci a kai. Muhammad Lawal ya yabawa gwamnatin jihar da tunanenta yana mai cewa a garesu su manoman shinkafa cigaba ne a wurinsu.
Amma wasu manoman sun koka akan tsadar wasu kayan da aka basu. Rijiyar da aka basu akan N15,000 su kan hakata akan N6,000 k0 N7,000. Iri da aka basu sukan sayoshi N3,000 amma gashi an basu akan N20,000.
Gwamnatin jihar tace shirin na gwaji ne kuma dorewarsa da fadadashi ya ta'allaka ne akan irin nasarar da aka samu.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5