ZAMFARA, NIGERIA - Gwamnan jihar, Dakta Bello Matawallen Maradun ne ya bada umarnin dakatarwar a yammacin ranar Lahadi, inda ya nisantar da gwamnatin jihar daga batun Nadin Aliero.
Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna ya bada, ta bayyana cewa gwamna Matawalle ya nada kwamiti mai mutane shidda a karkashin shugabanci Honarabul Yahaya Chado Gora, don ya binciki dalilin da ya sa Sarkin yin wannan nadin.
Sanarwar ta bayyana cewa, Alhaji Mahe Garba Marafa, hakimin ‘Yan Doton, shi ne zai gudanar da harkokin mulki a masarautar.
Tun da farko kafin a yi nadin sai da shugaban karamar hukumar Tsafe, Aminu Mudi Tsafe ya bayyana cewa Ado Aliero dan asalin Tsafe ne, kuma a baya bayan nan ya taimaka wajan samar da kwanciyar hankali bayan sulhun da aka yi, wannan ya sa mai girma Sarkin Birnin ‘Yan Doton ya ga dacewar a dora masa nauyin sarauta don ya kara tabbatar da zaman lafiya a daukacin masarautar baki daya.
“A bisa wadannan dalilan ne suka sa Sarkin ‘Yan Daton Tsafe ya amince da nadin Ado Aliero a matsayin Hardon Fulanin,” a cewar Mudi.
Wasu ‘yan asalin masarautar ‘Yan Doton, sun shaida wa Muryar Amurka cewa bayan sulhun, Aliero ya samar da zaman lafiya har an fara noma a gonaki a yankin, a cewarsu ta hanyar sulhu ne kadai za a samu zaman lafiya.
‘Yan bindiga da dama a kan babura ne dai suka halarci bukin nadin Sarkin Fulanin Daji Aliero.
Saurari cikakken rahoton Sani Shu'aibu Malumfashi:
Your browser doesn’t support HTML5